Shugaban kasar Sudan ta kudu salva kiyar ya sanya hanu kan yarjejeniyar sulhu tsakaninshi da bangaren yan tawaye bayan da majalisar dinkin duniya tayi barazanar kakaba masa takunkumi.
Da yake bayani a lokacin sanya hannu ya nuna cewa yana da shakku game da hanyoyin da masu shiga tsakani suka bi wato shugaban kasar kenya da Uganda da pira ministan kasar Ethiopia wajen bukin sanya hannun , hakazalika da ma wasu ayoyin doka da yarjejeniyar ta kunsa musamman game da batun rabon madafun iko tsakanin gwamnati da yan adawa da sauran jami’iyun siyasar kasar, da kuma dakatar da bude wuta cikin sao’i 74.
Har ila yau daga cikin abin da yarjejeniyar ta kunsa akwai batun kwabe danmarar yan tawayen Darfur da kuma kafa gwamnatin hadinkan kasa acikin kwanaki 90 daga lokacin da aka rattaba hannun, kana kuma a girka kwamitin hadin guiwa da taimakon kungiyar tarayyar Afrika da zai gudanar da bincike kan laifukan yaki da bangarorin biyu suka tafka domin humukumta masu laifi,
Ana kama Wasu mambobi a cibiyar Ahlul baiti ta duniya guda biyu jim kadan bayan isaru kasar Masar daga kasar Iran.
Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaron kasar Masar sun tsare Dr Rasam Nafis da Sayyid Dahir Hashimi mambobi a cibiyar Ahlul bait ta duniya dake da hedkwata a birnin Tehran jim kada bayan isarsu filin saukar jiragen sama na kasa da kasa na kasar dake birnin alkahira, bayan sun halarci taron kasa da kasa na cibiyar Ahalul Baiti ta duniya karo na shida da aka kammala a nan birnin Tehran a makon da ya gabata .
Sai dai bayan tsaresu na yan sa’oi daga bisani an sake su tare da kwace dukkan kyaayyakin da suke dauke da su da kuma pasport dinsu, da yake ganawa da manema labarai bayan an sake su ya bayyana cewa kasar Masar ta koma kamar kafin 25 ga watan janeru na juyin juya halin da aka yi a kasar,
Tun a lokacin gwamnati da ta gabata mabiya mazhabar ahlul bait a kasar Masar suke fuskanta matsin lamba da tsangwama duk da yake cewa suna kakrin samar da fahimtar juna tsakanin mabiya mazhabbobi a kasar sabanin sauran yan salafiya da suke kokarin ganin an takurawa yan shia’a a kasar.288
Ana kama Wasu mambobi a cibiyar Ahlul baiti ta duniya guda biyu jim kadan bayan isaru kasar Masar daga kasar Iran.
Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaron kasar Masar sun tsare Dr Rasam Nafis da Sayyid Dahir Hashimi mambobi a cibiyar Ahlul bait ta duniya dake da hedkwata a birnin Tehran jim kada bayan isarsu filin saukar jiragen sama na kasa da kasa na kasar dake birnin alkahira, bayan sun halarci taron kasa da kasa na cibiyar Ahalul Baiti ta duniya karo na shida da aka kammala a nan birnin Tehran a makon da ya gabata .
Sai dai bayan tsaresu na yan sa’oi daga bisani an sake su tare da kwace dukkan kyaayyakin da suke dauke da su da kuma pasport dinsu, da yake ganawa da manema labarai bayan an sake su ya bayyana cewa kasar Masar ta koma kamar kafin 25 ga watan janeru na juyin juya halin da aka yi a kasar,
Tun a lokacin gwamnati da ta gabata mabiya mazhabar ahlul bait a kasar Masar suke fuskanta matsin lamba da tsangwama duk da yake cewa suna kakrin samar da fahimtar juna tsakanin mabiya mazhabbobi a kasar sabanin sauran yan salafiya da suke kokarin ganin an takurawa yan shia’a a kasar.